✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya nada Oluwatoyin Madein a matsayin sabuwar Akanta-Janar ta Kasa

Nadin nata zai fara aiki nan take.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Misis Oluwatoyin Sakirat Madein, a matsayin sabuwar Akanta-Janar ta Tarayya.

Shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Dakta Folasade Yemi-Esan, ta bayyana nadin Madein a ranar Juma’a a Abuja.

A cikin sanarwar mai dauke da sa hannun daraktan yada labarai na ofishin shugaban ma’aikatan tarayya, Mohammed Abdullahi Ahmed, nadin Madein ya fara aiki daga ranar Alhamis, 18 ga watan Mayu, 2023.

“Sabuwar wadda aka nada za ta fara aiki nan take,” in ji shi.

Madein za ta maye gurbin Mista Sylva Okolieboh, wanda ya maye gurbin Idris Ahmed daga mukaminsa bisa zargin almundahana da almubazzaranci da dukiyar gwamnati.

A yanzu haka dai Ahmed na fuskantar shari’a bisa zargin almundahana da dukiyar al’umma.