✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya nada Obinna a matsayin sabon Shugaban PPPRA

Nadin zai fara aiki nan take kamar yadda Femi Adesina ya sanar.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Mista Atuonwo Obinna a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Farashin Albarkatun Man Fetur ta Kasa (PPPRA).

Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da mai ba wa Shugaban Kasa shawara kan kafofin watsa labarai, Femi Adesina, ya fitar a Abuja.

  1. ‘Gandun kiwon Dukku a Gombe zai rage rikicin manoma da makiyaya’
  2. Tabbas mun gayyaci Sheikh Gumi —DSS

Sanarwar ta ce nadin na Obinna a matsayin sabon Shugaban PPPRA ya yi daidai da sashe na 2(1-3) da sashe na 3 (a) na Hukumar Kula da Farashin Albarkatun Man Fetur din, na 2023.

Adesina ya kara da cewa Shugaba Buhari ya kuma amince da sake nada Abdulkadir Saidu a matsayin Sakataren Hukumar na tsawon shekara hudu.

Kamfanin Dillacin Labarai NAN, ya ruwaito cewar nadin na sabon shugaban zai fara aiki nan take.