Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Mohammed Hassan Abdullahi a matsayin sabon Ministan Muhalli.
Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha ne ya bayyana nadin nasa a cikin wata sanarwa a ranar Laraba.
- NDLEA ta kama ‘sarauniyar kwaya’ a Taraba
- Za mu gudanar da zaben fitar da ’yan takara a watan Mayu —APC
Sanarwar ta ce: “Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nada Mohammed H. Abdullahi a matsayin sabon Ministan Muhalli daga ranar 6 ga Afrilu, 2022.”
Mohammed Hassan Abdullahi wanda lauya ne kuma dan asalin Jihar Nasarawa, shi ne Karamin Minista Ma’aikatar Kimiyya da Fasaha kafin nada shi babban minista.