Jam’iyyar APC a Jihar Adamawa ta dakatar da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, saboda ya sha kasa a hannun jam’iyyar PDP a lokacin zabukan da suka gabata.
Jam’iyyar ta ce Boss Mustapha bai bayar da gudunmawar nasarar da ’yan takarar Shugaban Kasa da na Gwamna na APC suka samu a lokacin da ake bukatar taimakonsa ba.
- An ga watan Ramadan a Najeriya – Sarkin Musulmi
- Injiniyan Najeriya ya kera motar da za ta iya tashi sama a Borno
Da yake sanar da dakatarwar a wani taron manema labarai a Yola, babban birnin Jihar, Shugaban gundumar Gwadabawa, Mu’azu Kabiru, ya ce Boss Mustapha bai jajirce wajen samun nasarar APC ba a zabukan.
Ya ce bisa wasu korafe-korafe da ake yi masa, shuwagabannin jam’iyyar ta yanke shawarar dakatar da shi har abada tare da cewa kada daidaikun mutane su dauki kansu sama da jam’iyyar da ta ba su dama.
Shi ma Sakataren jam’iyyar APC na Gwadabawa, Abdulkarim Nuhu, ya ce sun yanke wannan hukuncin ne kasancewar yadda Boss Mustapha ke kauce wa a gansa koda an zo wajensa neman taimako ya kuma kara da cewa wannan shawarar su da mambobinsu ne baki daya suka yanke.