Matar da ta wallafa littafi a kan matar Shugaban Kasa, Aisha Buhari ta zama Wakiliyar Najeriya a Hukumar Ilimin Kimiyya da Al’adu ta Majalisar Dinkin Duniya (UNESCO).
Shugaba Muhammadu Buhari ya daga likafar Hajo Sani ne mako guda bayan kaddamar da littafin ‘Aisha Buhari: Being Different’, da ta wallafa a kan matarsa, a Fadar Shugaban Kasa.
- Abubuwan da ba a sakaci da su a Ramadan —Sheikh Daurawa
- Ban mutu ba, dogon suma na yi —Ummi Zee-zee
- Gwamnati ta ciri biliyan N57 daga CBN a asirce —Majalisa
- Na rabu da mai neman aurena kan raina Kwankwaso —Budurwa
Kafin nadin nada, Hajo Sani ita ce Mashawarciya ta Musamman ga Shugaban Kasa a kan Harkokin Mata.
Sanarwar kakakin Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya Ben Bem Goong, ya fitar ta kuma hada da wasu nade-nade da Shugaban Kasar ya yi a bangaren ilimi.
Sun hada da:
Farfesa Ibrahim Muhammad, Darakta, Zauren Harshen Larabci na Najeriya, Ngala, Jihar Borno.
Farfesa Abdullahi A. Abba, Uban Jami’ar Kimiyyar Lafiya ta Tarayya, Otukp, Jihar Binuwai.
Farfesa Idris Muhammad Buhaji, Babban Sakatare, Hukumar Kula da Ilimin Fasaha da Kere-kere, Kaduna.
Farfesa Paulinus Chijikoke Okwelle, Babban Sakatare, Hukumar Kula da Kwalejojin Ilimi, Abuja.
Farfesa Okpako Enaohwo, Shugaban Kwamitin Amintattu, Hukumar Kula da Kwalejojin Ilimi, Abuja.
Dokta Benjamin Ogbole Abakpa Babban Sakataren Hukumar Kula da Ilimin Babbar Sakandare (NSSEC), Abuja