✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya nada Bello Koko a matsayin shugaban hukumar NPA

Sanarwar ta ce nadin na Bello Koko zai fara aiki ne nan take.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada Mohammed Bello Koko a matsayin sabon Shugaban Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya (NPA).

Ibrahim Nasiru, Babban Manajan sadarwa na hukumar, ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Legas ranar Talata.

Bello Koko, ya zama mukaddashin Shugaban hukumar ne a ranar shida ga watan Mayun 2021, bayan an dakatar da Hadiza Bala Usman.

Kafin nadin nasa a matsayin mukaddashin Shugaban na NPA, Bello Koko ya kasance Babban Daraktan Gudanarwa na hukumar.

Sanarwar ta ce nadin nasa a matsayin Shugaban hukumar zai fara aiki ne nan take.