BBC ta ruwaito cewa Atiku Abubakar ya wallafa hakan a shafinsa na Twitter, inda ya ce, abin da Shugaba Buhari ya yi na nuna cewa akwai hadin kai a Najeriya.
A ranar Laraba ne Shugaba Buhari ya amince da biyan fanshon ga jami’an ‘yan sandan da gwamnatin Najeriya ta yi wa afuwa tun a shekarar 2000 lokacin mulkin Shugaba Olusegun Obasanjo.
Wadannan jami’an sun yi aiki ne a ‘haramtacciyar’ kasar Biyafra a lokacin yakin basasar Najeriya da aka shafe watanni 30 ana yi. Amma tun da da aka musu afuwar ba a biya su komai ba.
A wata sanarwa da wata hukuma wadda ke kula da biyan fanshon ta fitar ta ce, za a biya mutum 162 yayin da mutum 57 kuma iyalansu ne za su karba a madadinsu a biyan farko da za a yi.
Hukumar ta kuma ce za a fara biyan farkon ne ranar Juma’a 20 ga watan Oktobar nan a birnin Enugu da ke Kudancin Najeriya.