✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya kirkiro sabuwar hukuma, ya nada shugabanta

Buhari ya kirkiro Hukumar Kare Bayanai ta Kasa (NDPB) tare nada Dokta Vincent Olatunji a matsayin shugabanta nan take.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kirkiro Hukumar Kare Bayanai ta Kasa (NDPB), tare da nada shugabanta.

Buhari ya ba da izinin ne bayan Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na Zamani, Farfesa Isa Ali Pantami, ya mika masa bukatar yin hakan a karkashin ma’aikatarsa.

Shugaban Kasar ya kuma amince da bukatar Farfesa Pantami ta nada Dokta Vincent Olatunji daga Jihar Ekiti a matsayin Kwamishina na Kasa kuma Shugaban NDPB nan take.

Kafin sabon mukaminsa, Doka Vincent shi ne Daraktan Gudanarwa ta Intanet a Hukumar Bunkasa Fasahar Zamani ta Kasa (NITDA)

Kakakin Ministan, Uwa Suleiman, ta ce, “NDPB za ta dora a kan nasarorin da aka samu a karkashin dokar tabbatar da kare bayanai ta kasa, sannan ta taimaka wajen samar da muhimman dokokin kare bayanai.”

Ta bayyana cewa ayyukan sabuwar hukumar sun hada da kare bayanai da kuma hana yi musu kutse da dai sauransu, wanda ya zo daidai da abin da kasashen da suka ci gaba suke yi.