A ranar Litinin Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin tsohon Shugaban Majalisar Wakilai, Dimeji Bankole da kuma tsohon Gwamnan Jihar Ogun, Gbenga Daniel a fadarsa ta Villa da ke birnin Abuja.
A kwanan nan ne bakin Shugaban Kasar suka sauya shekarsu ta siyasa inda suka koma jam’iyya mai ci ta APC.
- COVID-19 ta kashe dan takarar Shugaban Kasar Congo
- Ramadan: Sudais ya kaddamar da keken rabon ruwan Zam-Zam a masallatan Harami
A yayin da Bankole ya sauya sheka daga jam’iyyar ADP (Action Democratic Party), Gbenga Daniel ya koma jam’iyyar mai ci ne daga babbar jam’iyyar adawa a kasar ta PDP.
Gbenga Daniel shi ne Darekta-Janar na yakin neman zaben tsohon mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, wanda ya tsaya takarar Shugabancin Najeriya a babban zabe na 2019.
Aminiya ta samu cewa Shugaban riko kuma jagoran kwamitin sulhu na jam’iyyar APC, Mai Mala Buni wanda ke zaman Gwamnan Jihar Yobe, shi ne ya jagoranci tawagar da ta ziyarci Shugaban kasar a birnin Abuja.
Sauran ’yan tawagar kusoshin jam’iyyar da suka ziyarci shugaban kasar sun hada da Gwamnan Jigawa, Muhammad Badaru da kuma takwaransa na Jihar Kebbi, Atiku Bagudu.
Gbenga Daniel wanda ya yi zaman Gwamnan Jihar Ogun daga shekarar 2003 zuwa 2011, ya yi takarar da Mista Bankole wanda ya yi zaman Shugaban Majalisar Wakilan a tsakanin shekarar 2007 zuwa 2011.
Kamar yadda masu iya magana kan ce ‘ba a fafe gora ranar tafiya’, ’yan siyasa na ci gaba da shige-da-ficen neman madafar da za su kama yayin da guguwar babban zaben 2023 ta fara kadawa.