✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya kaddamar da sabbin takardun kudi

Buhari ya kaddamar da sabbin takardun N200, N500 da kuma N1,000 ne kafin fara taron Majalisar Zartawa ta Tarayya a Fadar Shugaban Kasa.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabbbin takardun Naira 200 da Naira 500 da kuma Naira 1,000 a safiyar Laraba.

Buhari ya kaddamar da takardun kudin ne gabanin fara taron Majalisar Zartawa ta Tarayya da ke gudana a Fadar Shugaban Kasa.

Hadiman Shugaban Kasa irinsu Bashir Ahmad, Buhari Sallau da kuma Bayo Omoboyiowo sun ta fitar da hotunan sabbin takardun kudaden ta shafukansu na Twitter.

Sabuwar takardar Naira 200 da Shugaba Buhari ya kaddamar a ranar Laraba, 23 ga Nuwamba, 2022. (Hoto: Fadar Shugaban Kasa).
Sabuwar takardar Naira 500 da Shugaba Buhari ya kaddamar a ranar Laraba, 23 ga Nuwamba, 2022. (Hoto: Fadar Shugaban Kasa).
Sabuwar takardar Naira 1,00 da Shugaba Buhari ya kaddamar a ranar Laraba, 23 ga Nuwamba, 2022. (Hoto: Fadar Shugaban Kasa).

 A ranar 15 ga watan Disamba mai kamawa ne dai sabbin takardun za su fara aiki kafa-da-kafada da wadanda ake amfani da su a halin yanzu.

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da ranar 31 ga watan Janairu, 2023 a matsayin ranar daina amfani da takardun Niara 200, 500 da 1,000 da ake amfani da su a halin yanzu.

Tuni dai ta sanar da al’ummar Najeriya tare da bukatar su da su kai kudaden da suke da su zuwa bankuna domin sauyawa da sabbin da Buhari ya kaddamar a ranar Laraba.

Gwamna Babban Bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele, a lokacin ga yake mika wa Shugaba Buhari sabbin takardun kudin. (Hoto: Fadar Shugaban Kasa).

CBN ya bayyana cewa a janye tsoffin takardun da amfani da su ne a hankali.

Idan ba a manta ba, batun sauya takardun kudaden dai ya tayar da kura, amma CBN da Shugaba Buhari suka ce babu gudu, babu ja da baya.

Kawo yanzu dai akwai masu kiraye-kiraye, ciki har da ’yan Majalisar Dokoki ta Kasa, da al’ummar makiyaya da ke neman a kara wa’adin daina amfani da tsoffin takardun.