✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya kaddamar da hanyoyin Naira biliyan 36 da Gwamna Masari ya gina 

A ranar Litinin da ta gabata ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya assasa ginin Jami’ar Sufuri ta farko a Najeriya, wadda za gina a garin…

A ranar Litinin da ta gabata ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya assasa ginin Jami’ar Sufuri ta farko a Najeriya, wadda za gina a garin Daura mahaifar Shugaba Buhari.

Tun a  watan Oktoban bara ne Gwamnatin Tarayya ta amince da fitar da kudi don gina jami’ar, kamar yadda Hukumar Kula da Jami’o’i ta Najeriya (NUC ) ta ce. Jami’ar wadda ta Gwamnatin Tarayya ce, in aka gina ta, za ta mayar da hankali ne a kan bincike da ci gaban bangarorin sufuri a Najeriya. Baya ga wannan ta Daura, za a sake gina wata irinta a garin su Ministan Sufuri Mista Chibuike Amaechi a  Jihar Ribas.

Za a kashe Dalar Amurka miliyan 50 (kimanin Naira biliyan 18,) wajen gina jami’ar kamar yadda Minista Amaechi ya ce.

Kamfanin Gine-Gine na kasar China (CCECC) ne zai yi aikin gina jami’ar. Makasudin gina jami’ar shi ne don ta cike gurabun rashin aikin yi a bangaren sufuri, kamar yadda Ministan ya ce. Har wa yau, Gwamnatin Tarayya na son horafr da mutanen da za su rika kulawa da layukan jirgin kasa na kasar nan kamar yadda ake kulawa da hanyoyin mota.

Bangaren sufuri na daga cikin abubuwan da gwamnatin Najeriya ke mayar da hankali a kansu tun bayan Shugaba Buhari ya hau mulki a 2015, musamman in aka lura da yadda ake kara gina hanyar dogo da gyara filayen jiragen sama. Kazalika da tura matasa kasar China don karanto fannin injiniyan layin dogo wadanda  ake sa ran su ne za su fara koyar wa a jami’ar da zarar an kammala ta a badi.

Gwamnatin Buhari ta ranto kudade daga China wadda take kan gaba wajen zuba hannun jari a Najeriya.

A wannan rana ta Litinin, Shugaba Buhari ya bude wasu hanyoyi da gwamnatin Jihar Katsina ta Aminu Masari ta gina a jihar a kan Naira biliyan 36 da miliyan 12 domin inganta sufuri a karkara a sassan jihar. Daga cikin hanyoyin da aka bude mai tsawon kilomita 28, ta taso daga garin Randa ta nufi Doguru ta wuce Gallu zuwa Kwanar Gwanti ta fado Shargalle.

A lokacin da yake yanke zaren bude hanyar, Shugaba Buhari ya jinjina wa Gwamna Masari kan irin wannan yunkuri tare da kirkiro wasu abubuwan ci gaban al’umma a jihar. Shugaba Buhari ya bukaci ya ci gaba da irin wadannan ayyuka na raya kasa da al’ummarta.

A lokacin da yake jawabi, Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari ya ce, tun daga hawa mulkinsa a 2015 zuwa 2019 ya bayar da kwangilar gina hanyoyi 18 masu tsawon kilomita 509, an kuma kammala 10 daga cikinsu inda Shugaban Kasa da kansa ya bude uku daga cikinsu wadda ya bude ita ce ta hudu. Shida na can na jiran budewa yayin da 8 ke bisa hanyar kammalawa.

Gwamna Masari ya ce, jimlar kudin da aka kashe wajen gina hanyoyin 18 su ne Naira biliyan 36 da miliyan 12. Ya kara da cewa, an kuma sake bayar da kwangilar gyaran wasu hanyoyi 10 tare da inganta su bayan lalacewar da suka yi, masu tsawon kilomita 307.60 a kan Naira biliyan 11 da miliyan 943. An kammala wasu daga ciki yayin da wasu suke gab da kammalawa.

Gwamna Masari ya ce, an bayar da kwangilar gina wasu hanyoyin karkarar na burji guda 39 masu tsawon kilomita 461 a kan Naira biliyan biyu da miliyan 831 wadanda duk an kusan kammala su. Domin kara bunkasa harkokin sufuri a Jihar Katsina, Gwamna Masari ya ce, gwamnatinsa ta sayo sababbin motoci bas-bas 25 ta mika wa Hukumar Sufuri ta Jihar don amfanar al’ummar jihar. Sai ya tabbatar wa Gwamnatin Tarayya a karkashin jagorancin Shugaba Buhari cewa, zai ci gaba da bayar da goyon baya tare da tallafi don ganin cewa an samu nasara a kan gina  sabuwar jami’a ta sufuri da za a gina a Daura.