✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya kaddamar da aikin titin jirgin kasa a Kano

Shugaba Buhari ya sauka a Unguwar Zawaciki.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya ziyarci birnin Kano don kaddamar da aikin titin jirgin kasa da zai tashi daga Kano zuwa Kaduna.

A ranar Alhamis ce kai tsaye wani jirgi mai saukar ungulu ya sauke Shugaba Buhari a Unguwar Zawaciki da ke Karamar Hukumar Kumbotso, inda aka kaddamar da aikin hanyar jirgin kasar.

  1. Majalisar Zamfara ta yi sammacin mataimakin gwamna
  2. Buhari zai kaddamar da aikin shekara 40 a Katsina

Tuni dai Gwamnatin Tarayya ta sanar cewa da zarar an kammala layin titin jirgin kasar zai hade da Kaduna da Abuja da kuma Jihar Legas.

Jihar Kano ta yi fice wajen kasuwanci, wanda hakan ya sa ake mata lakabi da ‘cibiyar kasuwanci’.

Amma yawancin ’yan kasuwa sun fi mayar da hankali wajen yin safarar hajojinsu ta hanyar amfani da motoci saboda jirgin sama ya yi tsadar daukar kaya daga wata jiha zuwa wata.

Mazanarta sun ce da zarar an kammala layin dogon za a samu saukin jigilar kaya da kuma karancin asarar dukiya da ake tafkawa ta hanyar sufurin motoci.

A watan Fabrairu, 2021 Gwamnatin Tarayya ta sanar da kudirinta na shimfida layin dogo da zai tashi daga Jihar Kano zuwa garin Maradi na Jamhuriyar Nijar, don bunkasa harkokin kasuwanci.