Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya isa birnin Ikko inda ya kaddamar da aikin layin dogo wanda zai tashi daga Legas zuwa Ibadan.
Buhari ya kaddamar da sabon aikin layin dogo wanda gwamnatinsa ta kammala mai tsawon kilomita 157 a tashar Jiragen Kasa ta Mobolaji Johnson da ke Ebutte Metta.
- Yaki da rashawa akwai wahala a mulkin farar hula — Buhari
- Matsalar Tsaro a Arewa maso Yamma ta kai ni bango — Buhari
Kazalika, shugaba Buhari zai kaddamar da aikin tashar Jiragen Ruwa ta Energy Nature Light Terminal a Tashar Apapa, a wani yunkuri na ci gaba da kaddamar da ayyukan tabbatar da tsaro na sufurin jiragen ruwa da ake kira Deep Blue Project.
A tashar ta Apapa, Shugaba Buhari ya kaddamar da jiragen sintiri na ruwa da na sama da kuma masu saukar ungulu, wadanda za su rika shawagi a teku domin magance matsalar ’yan fashi da sauran ayyukan laifi a tekun Najeriya.
Tare da Shugaban akwai Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo Olu da takwarorinsa na Oyo da Ekiti, Seyi Makinde da Kayode Fayemi.
Haka kuma, akwai Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi da Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Raji Fashola da wasu manyan jami’an gwamnati.