✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya je Maiduguri jajanta wa ’yan Kasuwar Monday

Buhari zai je Fadar Shehun Borno, inda zai jajanta wa ’yan kasuwar da suka yi asarar dukiyoyinsu a gobarar ta ranar Lahadi.

Shugaban Kasa Muhamamdu Buhari ya isa Jihar Borno, domin jajanta wa ’yan kasuwar da iftila’in gobora ta shafa a Kasuwar Monday da ke Maiduguri.

An wayi gari ranar Lahadi a Maiduguri da gobarar, wadda ta lakume dubban shaguna a kasuwar, wadda ita ce mafi girma a Jihar Borno da ma yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Ana sa ran a yayin ziyarar ta ranar Alhamis, Buhari zai je Fadar Shehun Borno, inda zai jajanta wa ’yan kasuwar da suka yi asarar dukiyoyinsu a gobarar ta ranar Lahadi.

Shugaban kasar zai kuma kaddamar wa wasu ayyuka da suka hada da rukunin gidajen da Gwamna Babagana Zulum  ya gina da wasu tituna a garin Maiduguri.

Sauran su ne Cibiyar Kula da Masu Cutar Kansa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri da kuma Tashar Iskar Gas ta kamfanin NNPC.