Shugaban Kasa Muhamamdu Buhari ya isa Jihar Borno, domin jajanta wa ’yan kasuwar da iftila’in gobora ta shafa a Kasuwar Monday da ke Maiduguri.
An wayi gari ranar Lahadi a Maiduguri da gobarar, wadda ta lakume dubban shaguna a kasuwar, wadda ita ce mafi girma a Jihar Borno da ma yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.
- ’Yan sanda na ci gaba da tsare Ali Madaki kan daukar bindiga a yakin neman zabe
- Na tabbata Tinubu zai kai Najeriya tudun-mun-tsira —Aisha Buhari
Ana sa ran a yayin ziyarar ta ranar Alhamis, Buhari zai je Fadar Shehun Borno, inda zai jajanta wa ’yan kasuwar da suka yi asarar dukiyoyinsu a gobarar ta ranar Lahadi.
Shugaban kasar zai kuma kaddamar wa wasu ayyuka da suka hada da rukunin gidajen da Gwamna Babagana Zulum ya gina da wasu tituna a garin Maiduguri.
Sauran su ne Cibiyar Kula da Masu Cutar Kansa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri da kuma Tashar Iskar Gas ta kamfanin NNPC.