Shugaba Muhammadu Buhari ya ba da tabbacin cewa Najeriya za ta ci gaba da taka rawar gani da bayar da gudunmuwarta wajen ganin ci gaban yankin Yammacin Afirka da kuma nahiyar Afirka baki daya.
Shugaba Buhari ya bayar da wannan tabbacin ne a Fadarsa ta Villa da ke birnin Abuja, yayin ganawa da tsohon Shugaban Kasar Mali kuma Shugaban farko na Hukumar Tarayyar Afirka, Farfesa Alpha Oumar Konare.
- Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta karrama Sheikh Abdulwahab Abdullah
- Wata cibiyar Musulunci a kasar Syria ta karrama Sheikh Sani Rijiyar Lemo
Konare ya ziyarci Shugaba Buhari inda suka tattauna batutuwan da suka shafi rikicin siyasar da ya dabaibaye kasar Mali a halin yanzu da kuma sauran batutuwa da suka shafin Yammacin Afrika da ma nahiyar baki daya.
Shugaba Buhari cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Mallam Garba Shehu ya fitar a ranar Laraba, ya yabawa Farfesa Konare dangane da sha’awarsa a kan shawarar da ya nuna kan lamuran da suka shafi ci gaban Yammacin Afrika.