Shugaba Buhari ya karbi bakuncin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan wanda shi ne wakili na musamman kuma mai shiga tsakani na ECOWAS a kasar Mali.
Buhari, a yayin ganawar da aka gudanar a Abuja, kan rikicin siyasa a kasar, ya yi kira ga bangarorin da su hada kai don samun zaman lafiya da hadin kan kasar.
- El-Rufai na cijewa za mu yi yajin aikin gama-gari —NLC
- Mata sun yi zanga-zangar neman a halasta karuwanci
A cewarsa, “Yanayin da ake cikin wanda mafi yawan sassan kasar ke hannun masu tayar da kayar baya na bukatar a yi yarjejeniya tare da maido da zaman lafiya, ba kara rura wutar rikicin ba.
“Ina kira ga duk masu ruwa da tsakin su hada kai domin samun zaman lafiya da tsaro a Mali.”
Wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina ya fitar ta ce Jonathan ya yi wa shugaban bayanin halin da ake ciki a Mali bayan ganawa da manyan ’yan siyasa a gabanin taron shugabannin ECOWAS a karkashin Shugabancin Shugaba Nana Akufo-Addo na kasar Ghana.
Ya kara da cewa taron shugabannin kasashen yankin ya zama wajibi don hanzarta samar da ingantacciyar hanyar warware matsalar da ke addabar kasar ta Yammacin Afirka.