Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da gwamnonin APC 22 gabanin babban zaben fid-da-gwanin shugaban kasa da jam’iyyar za ta yi daga ranar Litinin 6 zuwa Laraba 8 ga watan Yuni, 2022.
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu ya halarci ganawar da Buhari ya yi da gwamnonin.
- Shan sigari na kashe ’yan Najeriya 29,000 a shekara
- Zaben Nijar: Kotun ECOWAS ta yi fatali da karar Mahamane Ousmane
Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ne kadai bai samu halartar taron ba inda mataimakiyarsa ta wakilce shi.
Aminiya ta gano cewa an yi taron ne domin tattauna batun zaben fid-da-gwani na shugaban kasa da ke tafe da kuma bukatar samun matsaya guda tare da gwamnonin da shugabansu Gwamna Atiku Bagudu na Jihar Kebbi ya jagoranta.
Jam’iyyar APC ta dage zaben fid da gwanin Shugaban Kasa da ta tsara gudanarwa a tsakanin ranar Lahadi 29 da Litinin 31 ga Mayun 2022, zuwa Litinin 6 da kuma Laraba 8 ga watan Yunin 2022, bayan da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta kara wa’adin gabatar da jerin sunayen masu neman takara.
Tuni shugaba Buhari ya bar Najeriya zuwa birnin Madrid na kasar Spain domin ziyarar aiki ta kwana biyu a kasar.