✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya gama lalata rayuwar ’yan Najeriya —Bishop Kukah

Yau ’yan Najeriya basa iya gane kasarsu saboda yadda ta fita daga cikin hayyacinta.

Babban Limamin mabiya darikar Katolika da ke Sakkwato, Bishop Mathew Hassan Kukah ya bayyana cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gama lalata duk wata madogara ta jin dadin rayuwar jama’a a kasar nan.

Haka kuma Bishop Kukah ya ce a karkashin gwamnatin Shugaba Buhari an bai wa cin hanci da rashawa damar habaka.

Yayin da yake gabatar da sakon bikin Easter a mujami’ar sa, Kukah ya ce duk wani bangaren rayuwar jama’ar Najeriya ya lalace, yayin da kasar ta zama sashen gobe da nisa na asibiti dauke da tarin marasa lafiya.

Limamin ya ce zukatan ’yan Najeriya tare da iyalansu da gidajen su da Majami’u da Masallatai da kayan more rayuwa duk sun ruguje a karkashin gwamnatin Buhari.

Kukah ya ce harkokin ilimin kasar ya ruguje tare da rayuwa da makomar yaran kasar kamar yadda bangaren siyasa da tattalin arziki da makamashi da al’ummomi da hanyoyin mota da na jiragen kasa suka rugeje inda babu abinda ke rayuwa yadda ake bukata da ya wuce cin hanci da rashawa.

‘Yan Najeriya basa iya gane kasarsu

Limamin ya ce yau ’yan Najeriya basa iya gane kasar su saboda yadda ta fita daga cikin hayyacin ta sakamakon matsalolin da suka mamaye ta a karkashin gwamnatin Buhari.

Kukah ya ce lura da irin wadannan dimbin matsalolin da suka addabi Najeriya wasu ’yan kasar na tambayar ko masu rike da madafun ikon a basa ji ko gani ko dandanar irin yanayin da jama’ar kasar suka samu kan su ne ko kuma suna nuna halin ko-in-kula ne domin babu abinda ya dame su.

Matakin sake dawo da kimar kasar

Limamin ya ce babban kalubalen da ke gaban jama’ar Najeriya a yau ita ce yadda za a fara daukar matakin sake dawo da kimar kasar da fatar mutane za su rayu har zuwa lokacin zaben shekara mai zuwa da kuma sanya ido akan abinda zai biyo baya domin fuskantar matsalolin da suka addabi kasar ta hanyar gina halayen jama’a da kuma son kasa.

Kukah ya bukaci shugabannin addinai da su tashi tsaye cikin gaggawa domin ceto Najeriya daga halin da ta samu kanta, musamman ganin yadda yanzu ake samun miliyoyin mutane a cikin kasar da duniya baki daya dake barin addinin Kirista da Musulunci domin zama marasa addinai.