✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari ya mika wa Majalisa kasafin 2021

Ya ware Naira 240 domin inganta rayuwa da kuma biliyan 20 na samar da gidaje

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce rashin samun kudaden shiga yadda ya kamata shi ne babban kalubalen gwamantinsa.

Da yake gabatar da kasafin 2021 a zauren Majalisar Tarayya ranar Alhamis, Shugaban Kasar ya bukaci Majalisar da ta ba da muhimmanci wajen sa ido a kan kudaden shigar gwamanti.

Ya ce tuni ya umarci ministocinsa da su tsaurara sanya ido kan hanyoyin tare kudaden shigar gwamnati.

Buhari ya ce an shirya kasafin kudin ne bisa la’akari da matsin da tattalin arzikin duniya ya shiga sakamakon bullar annobar COVID-19.

Ya ce kasafin ya ware Naira biliyan 240 domin shirin inganta rayuwar ‘yan Najeriya, da kuma Naira biliyan 20 domin samar da gidaje masu saukin kudi.

Kasafin kudin na Naira tiriliyan 13.08 ya kuma tanadi kudade domin ayyukan samar da wutar lantarki a karkara da kuma tashoshin lantarki na Mambilla, Zungeru da sauransu.

Abin da kasafin ya yi wa hukumomim gwamanti ya kai Naira biliyan 484.49, wadanda suka hada Kamfanin Mai na Kasa (NNPC), biliyan 29.7; Hukumar Kula da Ayyukan Shari’a ta kasa (NJC),  biliyan 110; sai Hukumar Kula da Ilimin Bai-daya (UBEC), biliyan N70.05.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) za ta samu biliyan N40; Majalisar Tarayya, biliyan N128bn, Hukumar Karbar Korafe-korafe ta Kasa (PCC), bilyan N5.2; Hukumar Kara Hakki ta Kasa (NHRC), biliyan N3bn dai hukumar lafiya, biliyan N35.03.

 

%d bloggers like this: