Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa Abuja, Babban Birnin Tarayya bayan ya shafe kwana takwas yana ziyarar aiki a kasar Saudiyya.
Yayin ziyarar, wacce fadarsa ta ce ita ce ta karshe zuwa kasar kafin karewar wa’adin mulkinsa, Buhari ya kuma yi Umarah a can.
- Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun hutun Sallah Karama
- Akwai fursunoni 3,298 da ke jiran a zartar musu da hukuncin kisa a Najeriya
Kakakin Shugaban, Malam Garba Shehu, wanda ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da maraicen Laraba, ya ce Buhari ya sauka a Abuja da misalin karfe 5:08 na yamma.
Sai dai Garba Shehu ya ce sai da jirgin Buhari ya shafe kusan awa bakwai kafin ya iso Najeriya saboda sai da ya kaurace wa bi ta kasar Sudan wacce a halin yanzu take fama da rikici.
Ya ce sai da jirgin da ya taso daga birnin Jiddah ya bi ta kasashen Eritrea da Habasha da Kenya da Uganda a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sannan ya bi ta Kamaru kafin daga karshe ya iso Najeriya.
Bayan isar tasa a filin jirgin sama na Abuja, Buhari ya sami tarba daga Shugaban Ma’aikatan Fadarsa, Farfesa Ibrahim Gambari da Mataimakin Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya, Danmallam Mohammed wanda ya wakilci Babban Sufeton da kuma Shugaban Hukumar Tsaro ta DSS, Yusuf Magaji Bichi.