✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya dawo hutun sallah har ya koma aiki

Shugaba Muhammadu Buhari ya koma bakin aiki a fadarsa da ke Abuja bayan hutun sallah da ya yi a garinsu Daura da ke jihar Katsina.…

Shugaba Muhammadu Buhari ya koma bakin aiki a fadarsa da ke Abuja bayan hutun sallah da ya yi a garinsu Daura da ke jihar Katsina.
A lokacin da yake garin Daura, Shugaban kasar ya yi sallar Idi tare da dubban Musulmi a filin Idi na garin a ranar Juma’a.
Shugaban kasar ya karbi tawagar kungiyar manoma da ta ’yan kasuwa da ta matasa da ta dattawa da kuma ’yan siyasa daga jihar Katsina inda ya basu tabbacin ci gaba da kara kaimi don bautawa kasarsa.