Shugaba Muhammadu Buhari ya dawo daga ziyarar aikin kwanaki hudu da ya kai biranen Ankara da Istanbul na kasar Turkiya.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa jirgin shugaban kasa ya tashi daga filin saukar jiragen sama na kasa da kasa na Ataturk da ke garin Istanbul da misalin karfe 12 na rana ya sauka a filin saukar jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da misalin karfe 4 da minti 5 na yamma.
Manyan jami’an gwamnati da suka hada da Shugaban Ma’aikata, Abba Kyari, da Sufeto Janar na ’Yan sanda, Idirs Ibrahim da Ministan Babban Birnin Tarayya, Alhaji Muhammad Bello da sauran masu taimakawa shugaban kasar sun tarbi Buhari tare da matarsa Aisha.