Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba wa Ministan Ilimi, Adamu Adamu, mako biyu ya kawo karshen yajin aikin da Kungiyar Malaman Jami’a (ASUU) ke yi.
Ya umarci Ministan da ya jagoranci zaman sulhun da gwamnati ta gayyaci ASUU domin sasantawa da ita da sauran kungiyoyin jami’o’i da ke yajin aiki.
- Zulum ya bai wa karamin yaro tallafin karatun N5m
- Kotu ta janye umarnin hana Ganduje karbo bashin N10bn
Ya kuma ba shi wa’adin mako biyu ya tabbata ya shawo kan duk matsalolin da suka hana sulhu da malaman jami’ar, sannan a kawo mishi rahoto.
Karin bayani na tafe…