✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya ce a ci gaba da amfani da tsoffin N200

Shugaba Buhari amince a ci gaba da amfani da tsoffin takardun N200 zuwa ranar 10 ga watan Afrilu.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba da izini a ci gaba da amfani da tsoffin takardun Naira 200.

Ya kara wa’adin amfani da tsoffin takardun N200 ne da kwana 60 zuwa ranar 10 ga watan Afrilu, 2023. Sannan ya ce cibiyoyin CBN za su rika amsar tsoffin takardun N1,000 da kuma N500 da ke hannun jama’a.

Buhari ya ba da izinin a ci gaba da amfani da tsoffin N200 ne ga Babban Bankin Najeriya (CBN) a yayin jawabinsa ga ’yan Najeriya a safiyar Alhamis.

Buhari, wanda ya bayyana cewa wahalar da canjin kudi ya jefa ’yan Najeriya ta dame shi, ya ce, “Domin saukaka halin da al’umma ke ciki, na amince wa CBN a ci gada da amfani da tsoffin N200 kuma bankuna su rika ba da su.

“Na kuma amince a ci gaba amfani da tsoffin takardun N200 din kafada-da-kafada da sabbin N200, sabbin N500 da kuma sabbin N1,000 na tsawon kwana 60 zuwa 10 ga watan Afrilu, ranar da tsoffin takardun N200 din za su daina aiki.”

Ya kuma tabbatar cewa cibiyoyin da CBN ya ware za su ci gaba da karbar tsoffin takardun Naira 500 da N1,000 da aka sauya daga hannun ’yan Najeriya.

A cewarsa, “A bisa tanadin Sashe 20(3) na Dake CBN ta 2007, Za a ci ga da karbar takardun Naira 500 da kuma N1,000 daga hannun jama’a a cibiyoyin CBN.”

Hakan na zuwa ne washegarin da Kotun Koli ta dage sauraron karar da wasu gwamnatocin  jihohi suka shigar na kalubalantar dokar haramta amfani da tsoffin N1,000 da N500 da kuna N200 da CBN ta canja.