Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bukaci ’yan siyasa da sauran ’yan kasa sun yi koyi da rayuwar Alhaji Balarabe Musa na rikon gaskiya da amana da kuma kishin kasa.
A takardar sanarwar da ya sanya wa hannu, Babban Mai Taimakawa Shugaban Kasa Kan Yada Labarai da Wayar da kan Jama’a, Malam Garba Shehu, ya ce Buhari ya yi kiran ne a sakonsa a wurin taron murnar cikar Balarabe Musa shekaru 81 a duniya.
Sanarwar ta nuna cewa Buhari ya kwatanta tsohon gwamnan jihar Kaduna da mutum mai kima wanda ya bar tarihi mai kyau a aikin gwamnati.