✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya bukaci sojoji su ci gaba da dagewa

Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci sojojin Najeriya masu yaki ’yan tada kayar baya da su ci gaba da dagewa kan kokarin da suke yi a…

Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci sojojin Najeriya masu yaki ’yan tada kayar baya da su ci gaba da dagewa kan kokarin da suke yi a yankin tafkin Chadi da sauran bangarorin Arewa maso Gabashin kasar.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a fadarsa lokacin da ya karbi bakoncin gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni.

Ya bayyana gamsuwarsa da nasarorin da sojojin suke samu a yaki da masu tada kayar baya, inda ya bukaci da su dage saboda kawar da kungiyar gaba daya.

Ya kuma gargadi sojojin akan sakaci wajen tsare yankunan kasar daga aiyukan ‘yan ta’adda.

“Hakan ya zama dole domin ganin harkokin noma da sauran aiyuka na yau da kullum basu fuskanci cikas ba, zaman lafiyar kasar ya dogara kacokan akan samar da isashen abinci.” Inji Buhari.

Shugaba Buhari, ya kuma bukaci gwamna Mai Mala Buni, da ya ci gaba bai wa sojojin hadin kai saboda samun nasarar aikin da suke yi.

A jawabinsa, Gwamna Buni ya yabawa gwamnatin tarayya akan kokarin da take yi na dakile hare-haren da ake kaiwa inda kuma ya ce sojojin sun samu gagarumar nasara a yankin.