Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bukaci Ministocinsa su ci gaba da rike mukamansu har zuwa ranar da za a rantsar da sabon Shugaban Kasa.
A ranar 29 ga watan Mayun 2023 ce Buhari zai mika ragamar mulki ga zababben Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu.
- Motar gidan sarautar Ingila ta kashe tsohuwa mai shekara 81
- Aikin jarida zan koma idan na sauka daga mulki – Gwamnan Binuwai
Akwai dai rahotannin da ke cewa Buhari ya sallami Ministocin a yayin taron Majalisar Zartarwa na bankwana da aka gudanar a Fadarsa da ke Abuja ranar Laraba.
To sai dai da yake zantawa da ’yan jaridar Fadar Shugaban Kasa bayan kammala taron, Ministan Yada Labarai da Al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya ce an umarci dukkan Ministocin su koma su ci gaba da ayyukansu a ma’aikatunsu.
Lai Mohammed ya ce, “Labarin da ake yadawa cewa an rushe Majalisar Ministoci ba gaskiya ba ne. Shugaban Kasa ya umarce mu mu ci gaba da aiki. Saboda haka ba a rushe mu ba, har yanzu muna nan.
“Labarin cewa an rushe mu karya ne. Na tabbatar za mu ci gaba da aiki har nan da ranar 29 ga watan Mayu. Saboda haka ku yi watsi da wancan labarin, ba shi da tushe ballantana makama,” in ji Ministan.