Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya bude sabon filin jirgin saman dakon kaya na kasa da kasa da ke Damaturu, babban birnin Jihar Yobe.
Shugaban, yayin ziyarar aiki ta kwana biyu da ya kai Jihar, ya kaddamar da sabon filin mai nisan kilomita 26 daga birnin na Damaturu, da sauran wasu ayyukan.
- Matar Shugaban DSS ta hana Abba Gida-Gida shiga jirgi daya da ita a Kano
- Ni na dora Bala a Gwamna, kuma ni zan sauke shi – Tsohon Wazirin Bauchi
Har ila yau, Buhari ya kuma bude ayyuka uku da Rundunar ’Yan Sanda ta Kasa ta gudanar a garin na Damaturu da suka hada da sabuwar hedkwatar ’yan sanda da makarantar yaran ’yan sanda sai kuma cibiyar kula da marasa lafiya ta jami’an ’yan sanda.
Sai dai Shugaban ya nuna mamakinsa kan yadda rundunar ta gudanar da wadannan ayyuka cikin kankanin lokaci.
Shugaban kasar ya kuma bude cibiyar kula da kananan yara da mata masu juna biyu da gwamnatin Jihar ta gina a harabar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jihar Yobe (YSU).
Ya kuma bude sabuwar kasuwar zamani da gwamnatin Yobe, karkashin Gwamna Mai Mala Buni ta gina a garin na Damaturu wacce ke cikin kasuwannin biyar da gwamnatin ta kaddamar da aikinsu daga hawan ta a 2019.
Sauran ayyukan da Shugaban Kasar ya bude sun hada da bude rukunin gidaje 2,350 musamman wanda ke kan hanyar Damaturu zuwa Potiskum da aka kammala su.
Ana sa ran Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai kwana a Damaturu babban birnin Jihar ta Yobe.
Sai dai har lokacin da ya kammala bude ayyukan, Shugaban bai ce komai ba, watakila sai daga baya duba da cewar a Jihar zai kwana.