✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya bayar da umarnin gano burtalan kiwo da aka mamaye

Ya bukaci a gano girman mamayar da aka yi wa dazukan na kiwo a kasar.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin ganowa da tantance burtalan kiwo 368 da ake da su a Jihohi 25 na kasar.

Hakan na kunshe cikin wata sako da mai magana da yawunsa, Mista Femi Adesina ya wallafa ranar Alhamis a shafinsa na Facebook.

Shugaban ya bayar da wannan umarnin ne bisa amincewa da shawarwarin da kwamitin da ya kafa kan burtalan kiwon karkashin jagorancin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari.

Sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar ta ce shugaban ya bukaci a gano girman mamayar da aka yi wa burtalan kiwo a kasar.

Daga cikin shawarwarin da kwamirin ya ba shugaban kasar sun hada da samar da taswirar dazukan da kuma tsara hanyoyin sadarwa da suka dace da ayyukan burtalan.

Sanarwar ta kuma ce hakkin kwamitin ne ya tantance matsayin dukkanin burtalan da halin da suke ciki na filayen da za a iya amfana da su.

Wasu daga cikin ’yan kwamitin sun hada da gwamna Abubakar Atiku Bagudu na Jihar Kebbi, da takwaransa na Jihar Ebonyi, David Umahi, Ministan Albarkatun Ruwa, Suleiman Adamu, Ministan Noma da Raya Karkara, Sabo Nanono da kuma Ministan Muhalli, Mohammad Mahmood Abubakar da sauransu.

Sauran mambobin kwamitin sun kunshi wakilai daga Ma’aikatar Shari’a, Hukumar Inganta Ayyukkan Noma da Filaye da Kasa NALDA, Hukumar Binciken Sararin Samaniya ta Kasa (NASRDA) da sauransu.