Gwamnatin Tarayya ta ayyana Litinin, 26 da Talata, 27 ga watan Disamban 2022 a matsayin ranakun hutu albarkacin bikin Kirsimeti na bana.
Gwamnatin ta kuma ayyana ranar Litinin, biyu ga watan Janairun 2023 a matsayin ranar hutun Sabuwar Shekara.
- Kotu ta tabbatar da Mohd Abacha a matsayin dan takarar Gwamnan Kano a PDP
- Tsohon Daraktan yakin neman zaben Gwamnan Gombe ya koma NNPP
Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, ne ya sanar da hakan a madadin Gwamnatin Tarayya a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Babban Sakataren ma’aikatar, Dokta Shuaib M.L. Belgore, a ranar Alhamis.
Ministan ya kuma taya ’yan Najeriya na gida da na ketare murnar, tare da yin kira a gare su da su yi koyi da kyawawan halayen Yesu Almasihu, musamman na imani da kaunar juna.
“Ya kamata mu yi koyi da halayen Yesu Almasihu na kaskantar da kai da tausayi da hakuri da son zaman lafiya tun daga lokacin haihuwarsa,” inji sanarwar.
Aregbesola ya kuma roki ’yan Najeriya da su yi amfani da lokacin wajen yin addu’ar samun dauwamammen zaman lafiya a kasar.
Ya kuma roke su da su tabbatar zaben 2023 an yi shi cikin lumana ta hanyar kauce wa duk wani abin da zai iya haifar da tayar da zaune tsaye ta kowacce fuska.