✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya ba ’yan Katsina hakuri kan matsalar ’yan bindiga

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba wa mutanen jihar Katsina hakuri a kan hare-haren ’yan bindiga da ke addabar jihar. A sakonsa na ta’aziyya ga…

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba wa mutanen jihar Katsina hakuri a kan hare-haren ’yan bindiga da ke addabar jihar.

A sakonsa na ta’aziyya ga wadanda hare-haren ya shafa, Buhari ya bukaci mutanen jihar da su ba wa sojoji hadin kai a yakin da suke yi da maharan, wadanda ya ce sojoji za su gama da su.

Sakon ta’aziyyar ya zo ne a lokacin da ayyukan mahara a jihar Katsina ke kara lakume rayuwa tare da jawo zanga-zanga da kiraye-kirage ga gwamnati ta yi wa tufkar hanci.

Sai dai Gwamna Aminu Masari ya amince da gazawar gwamnatinsa ta kare rayuka da dukiyoyi a jama’a, yana mai cewa ba zai iya yin ido hudu da wadanda hare-haren suka shafa ba.

A bangare guda kuma ana takaddama game da zargin da gwamnatin Buahri ta yi wa wasu sarakunan jihar na hada baki da maharan, lamarin da ya ja ‘yan jihar suka bukace ta da ta fallasa ta kuma hukunta sarakunan.

A sakon ta’aziyyar Buhari, babban mai taimaka masa kan yada labarai, Garba Shehu ya ce dakarun Najeriya na da karfin yakar maharan, don haka jama’ar da su daina boren da suke yi domin yana iya kawo tsaiko ga ayyukan da sojoji suke yi. Ya ce sojoji sun gano dazukan da maharan ke boyewa kuma za su fatattake su.

Makonni biyu baya sojoji sun kaddamar wani aiki a yankin Arewa maso Yamma da nufin yakar ‘yan bindiga a jihohin Katsina, Zamfara, Neja da Kaduna da kuma Sokoto.

Ko a makon jiya sai da daruruwa matasa a karamar hukumar Danmusa ta jihar Katsina suka gudanar da zanga-zangar nuna bacin rai game da karuwar hare-hare da satar mutane a yankin.

Hare-haren da na yankin Faskari na daga cikin mafiya muni a bayan-bayan nan wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar kusa mutum 100.