✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya bai wa ’yan Neja Delta 123,000 aikin tallafi

Masu amfana da tallafin sun fito ne daga kananan hukumomin yankin karkashin shirin daukar kananan ma'aikatan wucin gadi 1,000 a kowace karamar hukuma

Gwamnatin Tarayya a ce mutum 123,000 ne ke cin moriyar shirin bayar da tallafin Shugaba Buhari a yankin Kudu maso Kudu, wato Neja Delta.

Minista a Ma’aikatar Kudi da Kasafi da Tsare-tsaren Kasa, Prince Clems Agba, ya ce an zabo masu amfana da tallafin ne daga kananan hukumomin yankin 123 karkashin shirin daukar kananan ma’aikatan wucin gadi 1,000 a kowace karamar hukuma.

Da yake bayani gabanin tattaunawarsa da masu cin gajiyar shirin, Prince Clems ya ce, “Shirin na daga cikin yunkurin Shugaba Muhammadu Buhari na rage wa ‘yan Najeriya radadin illar COVID-19 ga tattalin arzikinsu kamar yadda bullar annobar ta girgiza tattalin arzikin gwamnatoci da kamfanoni da daidaikun mutane a fadin duniya.”

“Idan aka ninka yawan kananan hukumomin yankin Neja Delta da mutum 1,000 da suka ci gajiyar wannan shiri,” za a samu mutum 123,000, baya ga Naira biliyan daya da Gwamnatin Tarayya ta ware wa yankin Kudu maso Kudu na gyaran hanyoyi.

Ministan ya ce a karkashin shirin da Hukumar Samar da Ayyuka ta Kasa (NDE) take gudanarwa, ana biyan kowane mutum N20,000 a duk wata.