✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya ba sabbin gidajen rediyo da talabijin 159 lasisin fara aiki

Yanzu haka dai akwai kafafen yada labarai guda 625 a Najeriya.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ba sabbin gidajen rediyo da talabijin guda 159 lasisin fara yada shirye-shirye a Najeriya.

Wadanda aka ba lasisin dai sun hada kamfanoni da al’ummomi da kuma manyan makarantu.

Babban Daraktan Hukumar Kula da Kafafen Yada Labarai ta Kasa (NBC), Balarabe Ilelah ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a Abuja ranar Talata.

A cewarsa, “Bayan amincewar Shugaban Kasa, hukumar NBC ta fitar da sunayen kamfanoni da al’ummomi da kuma manyan makarantu wadanda aka ba lasisin fara yada shirye-shirye ta gidajen rediyo da talabijin.

“Dokar da ta kafa NBC a 2004 ta dora mata alhakin kula da harkokin kafafen yada labarai a Najeriya

“A yanzu haka, muna da kafafen yada labarai na rediyo da talabijin guda 625 a Najeriya,” inji Ilelah.

Shugaban hukumar ya ce tashoshin da aka ba lasisin sun hada da Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke Ilaro (rediyo) da mutanen ci gaban gundumar Reno (rediyo) da gidan rediyon al’umma na Smile da kuma Cibiyar Bincike kan Harkokin Noma ta Kasa da Kasa.

Ya ce sauran sun hada da kamfanin yada labarai na Dudu African, gidan talabijin na Independent da kamfanin Prince Media Network da Jamkat Integrity Investment Ltd da Hikima Media Services da kuma gidan rediyo da talabijin na Galaxy.

Sauran sune H-i Fidelity Communications da B360 Nigeria Ltd. da Communication Faculties Ltd. da gidan rediyon Jami’ar Godfrey Okoye da kamfanin Art Broadcasting da Hamdana Media da rediyon Sunshine da kamfanin jaridar Blueprint da dai sauransu. (NAN)