✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya ba da haquri kan matsalar qarancin fetur

A ranar Talatar da ta gabata ne Shugaban Qasa Muhammadu Buhari ya bai wa ’yan Najeriya haquri game da matsananciyar matsalar  qarancin man fetur xin…

A ranar Talatar da ta gabata ne Shugaban Qasa Muhammadu Buhari ya bai wa ’yan Najeriya haquri game da matsananciyar matsalar  qarancin man fetur xin da suke fama da ita.

Shugaba Buhari ya nemi gafara ne a lokacin da yake gabatar da qudurin kasafin kuxin baxi a zauren Majalisar Dokokin Qasar nan. Shugaban ya ce ya bayar da umarni ga hukumar da ke qayyade farashin man fetur da ta sake duba yadda take qayyade farashin man, yana mai umartar ta da ta tabbatar a yanzu farashin bai wuce Naira 87 kan kowacce lita guda.
Har ila yau, ya gabatar da kasafin Naira tiriliyan shida da biliyan takwas  a kan farashin kowacce gangar xanyen man fetur Dala 38 da kuma Naira 190 kan kowacce Dalar Amurka.
Hakazalika, Shugaban ya ce za a keve kashi 30 cikin 100 na kasafin kuxin domin gudanar da manyan ayyuka, sannan an ware kashi 70 cikin 100 domin yin ayyukan yau da kullum.
A vangaren manyan ayyuka, an keve wa Ma’aikatar Ayyuka da Makamashi da Gidaje Naira biliyan 433 da miliyan huxu; yayin da Ma’aikatar Sufuri ta samu fiye da  Naira biliyan 202; ayyuka na musamman Naira biliyan 200.
An keve Naira biliyan 396 ga fannin ilimi, yayin da aka ware Naira biliyan 296 ga kiwon lafiya, sannan an ware Naira biliyan 294 ga fannin samar da tsaro. Har ila yau, Shugaban ya bayyana cewa za a xauki malaman makaranta kimanin dubu 500 kuma gwamnati za ta xauki nauyin xaliban ilimin kimiyya da qere-qere da masu neman takardar shaidar koyarwa ta qasa kyauta.
Shugaban Qasar ya ce abin da ya sa gwamnati take biyan kuxin tallafin mai shi ne saboda Najeriya tana shigo da tataccen mai ne daga qasashen qetare duk da cewa  tana da arzikin mai. Ya ce ana ci gaba da kiraye-kiraye cire tallafi mai kuma abin da ya sa gwamnati ba ta xauki wannan matakin yanzu ba shi ne saboda kada gwamnati ta shiga taqaddama da qungiyar qwadago da kuma yadda masu qaramin qarfi za su shiga mawuyacin hali.
A qarshe Shugaban ya sha alwashin qwato dukkan kuxin Najeriya da aka sace, ko da kuwa hakan zai kai har qarshen wa’adin mulkinsa ne.