Shugaba Buhari ya karbi wayar salula ta farko da aka kera a Najeriya wadda aka sanya wa suna ITF Mobile.
Ministan Masana’antu da Kasuwanci, Otunba Adeniyi Adebayo ne ya kai masa daya daga cikin wayoyin gabanin fara taron mako-mako na Majalisar Zartarwar Kasa.
“An kaddamar da wayoyi 12 da cibiyar horarwar da take karkashin Ma’aikatar Masana’antu da Kasuwanci, ta kera su; Abin ya matukar kayatar da ni, da nake gabatar maka da daya daga cikin wayoyin ya Mai Girma Shugaban Kasa,” inji Ministan.
Ya ce wayar na daga cikin wayoyin da aka kera a Najeriyar ta hanyar amfani da kayayyakin hada ta da aka samar a nan gida wanda Sashen Lantarki da Laturoni na Asusun Bayar da Horon Ayyukan Masana’antu da Kere-kere ya kera.
Gabanin fara taron Majalisar Zartarwar, Shugaba Buhari, ya rantsar da kwamishinoni a Hukumar Kidaya ta Kasa da kuma Hukumar Aikin Gwamnatin Tarayya.