Shugaba Muhammadu Buhari ya gayyaci Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi kan Dala biliyan 16 na aikin jirgin kasa a kudancin Najeriya da sauran sassan kasar.
Yayin da yake yi wa manema labarai a fadar shugaban kasa jawabi, Amaechi ya bayyana cewa akwai abubuwan da suka taso dangane da harkar sufurin kasa da ya zama wajibi ya tattauna da shugaban kasa.
Ministan ya ce hawan jinin Shugaba Buhari zai iya tashi idan bai bayyana masa halin da bangaren sufurin kasar yake ciki ba.
Ya bayyana cewa gwamnatin ta amince da aikin dogon wanda zai tashi tun daga Fatakwal zuwa Maiduguri zuwa garin Aba da Owerri ta wuce zuwa Enugu da Umuahia ta bullo ta Makurdi zuwa Abakiliki ta bi ta Awka ta wuce Lafiya zuwa Bauchi zuwa Gombe zuwa Yola zuwa Damaturu ta kare a Barno.