✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari na tafiyar da Najeriya tamkar Rakumi babu akala —Tambuwal

Ya bayyana yadda ake tafiyar da Najeriya tamkar Rakumi babu akala.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sakkwato, ya bayyana Najeriya karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari da kuma jami’yyar APC a matsayin kasa maras alkibla. 

Tambuwal wanda ke zaman Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar PDP na kasa, ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai ranar Juma’a a Yenagoa, babban birnin Jihar Bayelsa.

A cewarsa, mummunan yanayin da ake ciki yanzu a Najeriya, ya sanya ’yan kasar ke ji tamkar babu wani mai jagorancinta, lamarin da ya bayyana Najeriya tamkar Rakumi da babu akala.

Tsohon Kakakin Majalisar Wakilan ya ce yadda ake tafiyar da Najeriya karkashin jagorancin jam’iyyar APC musamman a fagen rashin kulawa da al’amuran al’umma a halin yanzu ya sa ta doshi hanyar rugujewa.

Gwamnan na Sakkwato wanda yana daya daga cikin masu neman tsayawa takarar shugaban kasa a babbar jam’iyyar adawa ta PDP, ya bayyana damuwa kan yadda al’ummar kasar ke cikin mawuyancin hali karkashin jagorancin jam’iyyar APC.

Ya yi kira ga dukkan shugabannin jam’iyyar PDP, masu kishin kasa da masu da tsaki da suka kai don ganin an ceto kasar nan daga halin da take ciki.

Ya nanata cewa jam’iyyar PDP ce kadai za ta iya tsamo kasar nan daga halin da take ciki kuma ta kai ta zuwa tudun mun tsira.