✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari na son a yi gaskiya ne – Ogomo Pengana

Mai martaba Ogomo na Pengana da ke Qaramar Hukumar Bassa a Jihar Filato, Mista Esua Mamman Shayang, ya ce Shugaban Qasa Muhammadu Buhari mutum ne…

Mai martaba Ogomo na Pengana da ke Qaramar Hukumar Bassa a Jihar Filato, Mista Esua Mamman Shayang, ya ce Shugaban Qasa Muhammadu Buhari mutum ne da yake son a yi gaskiya a Najeriya. Ogomo na Pengana ya bayyana haka ne lokacin da yake zantaka da kakilinmu, inda ya ce, Shugaban Qasa Muhammadu Buhari yana son a yi gaskiya a Najeriya, don haka ya kamata  sauran shugabannin da aka zaba, a kkanakin baya su mara masa baya, kan kannan qudiri nasa, domin a gyara qasar nan.

Ya ce, manufofin Shugaban Qasa masu kyau ne, musamman manufarsa ta yaqi da cin hanci da rashaka kanda shi ne ya kashe qasar nan.

Ogomo na Pengana ya yi kira ga Shugaban Qasar ya qara daura damara kan samar da zaman lafiya a qasar nan. Domin idan babu zaman lafiya babu abin da za a iya yi.

“Sakamakon rashin zaman lafiyar nan arzikin qasar nan duk yana tafiya ne kan maganar tsaro. Don haka al’ummar Najeriya su nemi zaman lafiya da junansu, domin a samu damar yin abubukan ci gaba. Kamar bunqasa ilimi da kikon lafiya da harkokin noma,” inji shi.

Ya yaba ka al’ummar Najeriya kan yadda aka gudanar da zabubbukan Shugaban Qasa da gkamnoni da na majalisu lafiya.