✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari na jagorantar taron Majalisar Zartarwa

Zaman Majalisar Zartarwa na 19 ta fasahar zamani wanda Shugaba Buhari ke jagoranta

Majalisar Zartarwa ta Kasa ta fara zamanta na 19 wanda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ke jagoranta a ranar Laraba.

Taron da ke gudana a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja ya samu halarcin Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, Shugaban Ma’aikatan Fadar, Ibrahim Gambari da Mai ba da Shawara kan Tsaron Kasa, Babagana Monguno.

Ministan Watsa Labarai da Raya Al’adu, Lai Mohammed; Ministar Kudi, Zainab Ahmed; Ministan Shari’a Abubakar, Malami;  da Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola; da Ministan Tattalin Arziki na Zamani, Isa Ali Pantimi na daga jimin mahalarta zaman da aka fara da misalin karfe 10 na safe.

Sauran mahalarta su ne Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi; Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika; Ministan Harkokin Cikin Gida, Rauf Aregbesola, Ministan Lafiya, Osagie Ehanire; da kuma Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman.

Masu halartar taron ta bidiyo daga ofisoshinsu sun hada da Shugabar Ma’aikatan Gwamantin Tarayya, Folasade Yemi-Esan, da sauran ‘yan Majalisar ta Zartarwa.