Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gana da tsofaffin shugabannin kasa a fadarsa da ke Abuja.
Tsofaffin Shugabannin Kasa Olusegun Obasanjo, da Ibrahim Babangida, da Goodluck Jonathan, da Abdulsalami Abubakar, da Yakubu Gowon da Earnest Shonekan ne suka halarci taron da Buhari ya kira ya kuma jagoranta.
- Muhimman abubuwa 12 daga jawabin Buhari kan zanga-zangar #EndSARS
- A dakatar da Zanga-zangar #EndSARS —Shugabannin Kudu
Zaman nasu na zuwa ne washegarin jawabin Buhari ga ‘yan Najeriya game da zanga-zangar #EndSARS da ta rikide zuwa tashin hankali har da asarar rayuka da dukiyoyi a sassan kasar.
Sauran mahalarta su ne Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo; da Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha; da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Ibrahim Gambari; da Mai Ba da Shawara kanHarkokin Tsaron Kasa, Babagana Monguno.
Kazalika Manyan Hafsoshin Tsaro, da Shugaban ‘Yan Sanda da na Hukumar Tsaro ta DSS, da ta Tara Bayanan Sirri (NIA) sun halarci zaman na ranar Juma’a.
A safiyar ranar Alhamis Buhari ya jagoranci taron Majalisar Tsaro ta Kasa inda aka tattauna game da zanga-zangar ta #EndSARS.
A jawabinsa da dare, Buhari ya bukaci matasan da ke zanga-zangar da su daina, su zauna da gwamnati domin samun biyan bukatunsu da ya ce gwamantinsa ta yi nisa wajen biyan su.
Ya kuma jajanta game da rayukan da aka rasa a lokacin zanga-zangar, tare da nuna takaicin yadda bata-gari suka saje da masu zanga-zangar wajen aikata barna.