Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da gwamnonin Jam’iyyar APC guda 16 na halartar taron Kwamitin Zartarwar Jam’iyyar na Kasa a yanzu haka.
Tun da farko Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar na Kasa ya yi watsi da taron a matsayin haramtacce, tana mai cewa wanda ya kira taron Victor Giadom ba dan jam’iyyar ba ne domin kotu ta dakatar da shi daga jam’iyyar.
Duk da haka, bayan Buhari da gwamnoni, Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan da takwaransa na Majalissar Wakilai, Femi Gbajabiamila na daga cikin mahalarta taron wanda ake gudanarwa daga Fadar Shugaban Kasa.
Gwamnonin Nasarawa, Neja, Jigawa, Filato, Imo, Kogi , Yobe , Gombe , Osun , Ogun, Lagos , Kwara, Kebbi, Kano Ekiti, da Kaduna na daga cikin wadanda suka je fadar gwamnati domin halartar taron.
Kazalika wasu jami’ai da kusoshin Jam’iyyar wadanda su ma ‘yan kwamitin zartarwar ne na jam’iyyar.
Taron shi ne na farko da ake gudanarwa irinsa ta fasahar zamanin ta teleconferencing.
Gayyatar taron da Mataimakin Sakataren Jam’iyyar na Kasa Victor Giadom ya haifar da tayar da jijiyar wuya tsakanin bangarensa da ke samun goyon bayan gwamnoni da ɓangaren Uban Jam’iyyar na Kasa Bola Tinubu da Kwamitin Gudanarwa na Kasa a daya bangaren.
Jami’iyyar APC ta tsinci kanta a cikin rikicin shugabanci tun bayan dakatarwar da kotu ta yi wa shugabata na kasa Adams Oshiomhole.
Uwar Jam’iyyar na nada Abiola Ajimobi yayin da Giadom daga daya bangaren ya nada kansa a matsayin shugaban jam’iyya na riko.