✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari: Alkawari kaya ne (1)

Abubuwa da dama zan iya tunawa game da MUHAMMADU BUHARI, na farko dai shi BUHARI ba mazari ba ne da ba wanda ya san gabansa.…

Abubuwa da dama zan iya tunawa game da MUHAMMADU BUHARI, na farko dai shi BUHARI ba mazari ba ne da ba wanda ya san gabansa. BUHARI ba matsoraci ba ne, shi ya sa ko a fagen daga ake sayyare masa shugabancin dakaru. BUHARI mutum ne da idan ya tauna abu ya yarda da muhimmancin wannan abu, koda kuwa abin zai zame masa alakakai ko ya shafi na wani kusa da shi, in dai abin zai amfani al’umma, zai fuskance shi gadan-gadan. BUHARI mutum ne da ya tsare gaskiya, shi ya sa ba ya fargabar zargi ko zagi kan kowane lamari da ya samu kansa.

Wadannan batutuwa ni ganau ne ba jiyau ko sanau ba, shi ya sa zan iya tabbatar da hakan. Ga misali:
1. Ina daga cikin mutane da suka nuna rashin goyon bayansu a lokacin da BUHARI ya amince da ya karbi shugabancin PTF da Gwamnatin Tarayya ta mika masa. Tunanina da wasu irina shi ne, gwamnati za ta yi amfani da ganga ne ta jefar da kwaure; ma’ana, ganinsa a matsayin na kwarai za ta jawo shi jiki domin ta karu da shi daga baya ta yi watsi da shi, kila ma ta bata masa suna, domin shi ma ya bi layi. Ganin irin muhimmancin wannan aiki na PTF ya sa BUHARI ya karba, ya kuma yi iya gwargwadonsa, duk da cewa tunanina da na wasu irina ya so bayyana, a inda aka rika lakaba masa zarge-zarge har zuwa yau game da almundahana a lokacin yana shugabancin PTF, duk kuwa da cewa ba gaskiya a zarge-zargen.
2. Haka kuma a lokacin da BUHARI ya kammala shugabancin PTF ya dawo gida, ina daga cikin kalilan da suka samu tattaunawa da shi na awoyi, na kuma sake tada zancen zamansa shugaban PTF da takaddamar da ta biyo bayan barinsa na neman bata masa suna. Abin da ya fada min shi ya fi burge ni, ya ce, “Idan da za a sake nemana na sake yin irin wancan aiki na PTF, zan sake amsa na yi shi iyakar karfina, domin kuwa jama’a za a yi wa aiki.” Wannan ya kara tabbatar mini da cewa ba abin da ke tattare da shi, irin a yi wa jama’a aiki.
3. A lokacin da ya soma takarar neman Shugabancin Najeriya, mun yi rubutu da muka sa wa suna SHINGAYEN DA KE GABAN BUHARI, inda muka lissafo abubuwan da muke ganin cewa su ne za su hana shi ya kai gaci. Na kai wa BUHARI wannan rubutu da aka buga a jarida har cikin gidansa, muka zauna, ya nazarci rubutun, ya dube ni ya ce, “Kana kuwa tare da mu kake irin wannan rubutun?” Nan take na nuna masa ruhin yin wannan rubutu, na ce tamkar littafin dabashiri ne da zai iya aiki da shi ya kai ga nasara. Ya kuma bi matakin ganin ya kauce wa wasu daga cikin wadannan shingaye, duk da ba a yi nasara ba.
4. Abu na karshe shi ne, duk da cewa ba wani abu da zai tsinto a fadar Shugabancin Najeriya ta Aso Rock, wato irin batun nan da Hausawa ke cewa wane irin dare ne jemage bai gani ba, BUHARI bai fasa yin tsayin daka domin ganin jam’iyyarsa da ya gina bisa akidar ceto talaka da Najeriya ta ci zabe ba. Ga BUHARI, ba wai dole sai shi ya yi takara ba, a’a, ya dai ga an samar wa kasar nan mafita daga mugayen ungulai da ke mulkarta. Shi ya sa koda talakawa daga kowane bangaren Najeriya suka dage cewa SAI BUHARI, ya amince ya ci gaba da takara, duk da cewa ya haye shekara 70, wanda yake lokacin hutu ne ga mutum irinsa.
Wadannan misalai da wasu da dama su ne suka sa nake da yakinin cewa dukkan alkawarin da BUHARI ya yi a lokacin fafutikar neman Shugabancin kasar nan, zai cika su, domin ban san shi da yin alkawarin da ya sani a cikin ransa bai yiwuwa, ya kuma dage cewa sai ya yi ba. Na kuma hakikance cewa in har ya ga alamun ba zai iya cika alkawari ko gwamnatinsa ba za ta iya kai gaci kan wata matsala ba, zai bayyana wa jama’a hakikanin gaskiya, da abin da ya dace a yi!
Wannan tunani da na dade tare da shi game da BUHARI shi ne ya kasance linzamin wannan rubutu da zan fara daga yau har ranar da aka kammala zaben Shugaban kasa a ran 14 ga Fabrairu na 2015 da ma bayan nan, wato koda Buhari ya ci zabe, In Allah Ya so. Abin da zan yi a nan shi ne, in fasalta alkawurran da BUHARI ya yi domin a zabe shi Shugaban kasa da matakan da gwamnatinsa za ta bi domin ganin kwalliya ta biya kudin sabulu, in ta dare bisa karagar mulki nan da 29 ga watan Mayu na shekarar 2015, in Allah Ya kai mu!
Abin da nake so mu yi amanna da shi a nan shi ne, zaben BUHARI Shugaban kasa, zaben nagari ne, ina kuma da yakinin bisa ga dukkan alamu, zaben BUHARI turba ce ta ci gaba da sake fasalta ci gaban tsarin Shugabancin kasar nan da yardar Allah.
ME BUHARI ZAI IYA YI GAME DA ALMUNDAHANA DA LALACEWAR SHUGABANCI A NAJERIYA?

Za mu ci gaba.