✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari a Indiya

A makon da ya wuce ne Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci taron hadin gwiwar Indiya da Afirka karo na uku, inda mahalarta suka fito daga…

A makon da ya wuce ne Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci taron hadin gwiwar Indiya da Afirka karo na uku, inda mahalarta suka fito daga kasahen da ke cikin nahiyar Afirka dandamalin tattaunawar Indioya da Afirka, wanda aka yi wa lakabin IAFS, shi ne  wurin kulla alakar afirka da Indiya da aka amince da shi a hukumance Cibiyar ta IAF na gudanar da taronta a bayan kowace shekara uku. An kuma fara gudanar da wannan taro ne birnin New Delhi cikin shekarar 2008. Taron ya kasance irin san a farko d aya samu halartar daukacin shugabannin kasashen nahiyar Afirka 14 da Tarayyar Afirka ta zabo su. A karo na biyu kuwa an gudanar da taron ne a kasar Habasha, cikin shekarar 2011.
Buhari ya yi muhimmin bayani a lokacin ziyararsa. Ya yi nuni da tabbaci, alal m,isali cewa taron Indiyawa da ’yan afirka zai kara bunkasa hadin gwiwa tsaskanin kasashen Kudu, watao kasashe masu tasowa. Indiya da Afirka, a cewar Buhari dole su fahimci cewa sun zamo tsoka da jiki a wannan duniya da take a tarwatse, sannan su inganta ruhin sadaukar da kai da hadin gwiwa da hada karfi wajen tunkarar barkazanar da ke tasowa.
Ya ce: “dole ne mu yi aiki tare wajen daukaka darajar mutanenmu ta hanyar bai wa muhallinmu kariya mai dorewa. Irin wadannan kalublen na nuni da bukatar da ake da ita ta gaggawa wajen kara azama a tasakanin kasashen Afirka don bunkasa tatalin arziki. Al’amari ne da ke bayyane karara, Afirka ta mallaki duk abin da ake bukata don bunkasa wannan sashe na duniya.”
Ya ce duk da cewa kasashen Afirka sun kulla dangantakar hadin gwiwa da dama da sauran kasashen duniya, dandamalin hadin gwiwar Indiya da Afirka ya sha alwashin bambanta da sauran,” domin ba hadin gwiwa ce kawai ba a tsakanin abokai, a’a, tsakanin tsakanin kasashe da mutanensu, wanda ke da tarihi iri guda kan abin da ya shafi mulkin mallaka.” Ya ce, dimbin albarkatun da wannan dandamali ya tattaro, al’amarin da ke nuni da tumbatsa da kasurar ka’idojin kasuwanci da aka gindaya tsakanin Afirka da Indiya, tare da karuwar kamfanonin Indiya a Afirka.
Shugaba Buhari ya yi amfani da wannan damar taron ya bayyana shirin da yake yi wa Najeriya. Ya ce:”Ya ce za a ci gaba da yaki da cin hanci da rashawa twsawon shekaru. Mun jajirce wajen samar da shugabanci nagari, don toshe kafofin dibar kudi a ma’aikatun gwamnati, don alkinta albarkatun da muke da su wajen kyautata rayuwar al’umma. Mun dage wajen nuna misali a jagoranci, ta yadda za mu sanya al’ummarmu ta sauya tsarin rayuwarta, wajen kafa tushen gyara da bunkasar ci gaba.
“Ina da tabbacin cewa hanyar da muka dauko ta yakin da cin hanci da rashawa, ta hanyar gyaran tarbiyya da inganta tsarin ayyuka a cikin gida da bin doka, da inganta hukumomin yaki da cin hanci da rashawa, za su tabbatar da cewa fafutikarmu tad ore wajen shawo kan wannan mummunar dabi’a. Baya ga haka za mu ci gaba da gurfanar da wadsanda aka same su da aikata cin hanci da rashawas, ta yadda za a kwato kudin da suka sace, kuma ya zama darasi ga wadanda ke kokarin samun mukamin gwamnati don cimma bukatun son ransu.”
Dangane da abin da ya shafi tattalin arziki kuwa, shugaban ya ce gwamnatinsa, za ta warware matsalolin samar da kayan more rayuwa dungurugum, musamman al’amarin da shafi wutar lantarki da harkar sufuri. A cewarsa: “Muna kokarin samar da ayyukan yi a fannonin da suka hada da aikin gona da hakar ma’adinai da kafa masana’antu da daukaka kananan masana’antu.”
Wani sharhi da buhari  ya yi a hirarsa da tashoshin talabijin din NTA da Channel kafin ya bar birnin New Delhi ya dusashe hasken ziyararsa. Tunda a hirar ya yi bayanin cewa wasu daga cikin ministocin da aka tantance a majalisar dattijai ba za su samu gafaka ba, saboda Najeriya ta “talauce” sannan “babu kudin da za a biya su. “ Kalaman Buhari masu nauyi da ya yi a wajen kasar nan ci gaba ne da al’adar nan ta bayyana muhimman al’amaura a kasashen waje. Domin a lokacin ziyarar da ya kai Amurka, ya bijiro da wani babban al’amari game da yaki da cin hanci da rashawa, da kuma manufarsa ta zama ministan albarkatun man fetur. Wannan al’amari na bukatar a sake nazarinsa. Domin kada a fahimci cewa kasashen waje na kambama tunanin shugabanninmu su rika bayyana abubuwan da suka shafe mu fiye da yadda za su fada a Najeriya.