✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

BUGOM: Tsohon dan Majalisar Wakilai Daga Yobe Ya Rasu

Marigayi Goni shi ne tsohon mai wakiltar Bursari/Geidam/Yunusari a Majalisar Wakilai

Allah Ya yi wa tsohon dan Majalisar Wakilai kuma Kwamishinan Harkokin Matasa da Wasanni na Jihar Yobe, Goni Lawan Bukar, rasuwa.

Goni wanda shi ne tsohon mai wakiltar Bursari/Geidam/Yunusari a Majalisar Wakilai, ya rasu ne a sanadiyyar hatsarin mota a kan hanyar Damaturu zuwa Kano.

Wata majiya ta kusa da iyalinsa ta tabbatar da rasuwarsa a ranar Talata, da cewa “A huta lafiya, Goni Lawan Bukar, BUGOM”.

Marigayi Goni Bukar, wanda aka fi sani da BUGOM, ya yi aiki a matsayin kwamishina a Gwamnatin Mai Mala Buni bayan ya kasa komawa ga Majalisar Wakilai a 2019 sakamakon maye gurbinsa da aka yi da wani dan takarar.

A baya ya kasance Kwamishina a Ma’aikatar Filaye, Safiyo da Ma’adanai kafin daga bisani ya zama dan Majalisar Wakilai inda ya rike mukamai da dama a kwamitocin daban-daban na Majalisar.