Allah Ya yi wa tsohon dan Majalisar Wakilai kuma Kwamishinan Harkokin Matasa da Wasanni na Jihar Yobe, Goni Lawan Bukar, rasuwa.
Goni wanda shi ne tsohon mai wakiltar Bursari/Geidam/Yunusari a Majalisar Wakilai, ya rasu ne a sanadiyyar hatsarin mota a kan hanyar Damaturu zuwa Kano.
- Haramta yin acaba zai kawo karuwar ta’addanci —Masu babura
- DAGA LARABA: ‘Ina Sayar Da Kwalaba 1,000 Na ‘Kurkura’ a Mako A Zariya’
Wata majiya ta kusa da iyalinsa ta tabbatar da rasuwarsa a ranar Talata, da cewa “A huta lafiya, Goni Lawan Bukar, BUGOM”.
Marigayi Goni Bukar, wanda aka fi sani da BUGOM, ya yi aiki a matsayin kwamishina a Gwamnatin Mai Mala Buni bayan ya kasa komawa ga Majalisar Wakilai a 2019 sakamakon maye gurbinsa da aka yi da wani dan takarar.
A baya ya kasance Kwamishina a Ma’aikatar Filaye, Safiyo da Ma’adanai kafin daga bisani ya zama dan Majalisar Wakilai inda ya rike mukamai da dama a kwamitocin daban-daban na Majalisar.