✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buffon da Messi da Ronaldo ne za su fafata a Gasar UEFA ta bana

Hukumar shirya kwallon kafa a Nahiyar Turai (UEFA) ta zabo ’yan uku da suka kasance a sahun farko wanda za su fafata a Gasar Gwarzon…

Hukumar shirya kwallon kafa a Nahiyar Turai (UEFA) ta zabo ’yan uku da suka kasance a sahun farko wanda za su fafata a Gasar Gwarzon dan kwallon da ya fi nuna kwazo a bana.

’Yan kwallon da za su fafata a kokarin lashe wannan kyauta su ne golan kulob din Jubentus na Italiya Gianluigi Buffon na Italiya da Lionel Messi na FC Barcelona da ke Sifen da kuma Cristiano Ronaldo na kulob din Real Madrid na Sifen.

Hukumar ta ce za ta sanar da wanda ya lashe wannan kyauta ce a ranar Alhamis 24 ga watan nan da muke ciki a lokacin da za a fitar da Jadawalin Gasar Zakarun Kulob na Turai (Champions League) a hedkwatar Hukumar da ke Nyon na Switzerland.

Sauran ’yan kwallo 10 da hukumar ta zaba tun da farko sun hada da Luka Modric na kulob din Real Madrid da Toni Kroos shi ma daga kulob din Real Madrid sai Paulo Dybala na kulob din Jubentus na Italiya.  Sauran sun hada da Sergio Ramos na kulob din Real Madrid da Kylian Mbappe na kulob din Monaco da ke Faransa sai Robert Lewandowski na kulob din Bayern Munich na Jamus da kuma Zlatan Ibrahimobic na kulob din Manchester United.

Kimanin shekara 6 kenan da Hukumar UEFA take gudanar da irin wannan gasa kuma Lionel Messi da Cristiano Ronaldo ne ’yan kwallon da suka taba lashe kyautar sau biyu.

A bana ana sa ran Ronaldo ne zai lashe kyautar a karo na uku ganin yadda ya taimaki kulob din Real Madrid wajen lashe kofin zakarun kulob na Turai a karo na biyu a jere.