A ranar Talatar da ta wuce ne shahararren dan kwallon Real Madrid na Sifen kuma haifaffen kasar Wales Gareth Bale ya baza hoton ’yar da budurwarsa mai suna Emma Rhys-Jones ta haifa masa a karo na biyu a kafar sadarwarsa ta Instagram da kuma Twitter.
dan kimanin shekara 26 ya bayar da wannan sanarwar ce jim kadan da samun hutun mako daya daga kulob din Real Madrid da kuma kasarsa ta Wales saboda haihuwar da aka yi masa.
Wannan haihuwar ta sa dan kwallon ba zai buga wasannin sada zumuntar da Wales za ta yi da Northern Ireland da kuma Ukraine ba.
Bale dai ya watsa hoton jaririyar ce da ya rada mata suna Naba balentina a kafar sadarwarsa ta Instagram da Twitter inda aka ga ya rike wa jaririyar hannu tare da sakon “ina farin cikin sanar da ku samun karuwar ’ya mace wacce na rada wa suna Naba balentina”.
Naba dai a yaren Hebrew na nufin abin kauna, ko farin ciki ko kyakkyawa.
Gareth Bales dai yana zaune ne a Sifen tare da budurwarsa Emma Rhys-Jones bayan ya koma kulob din Real Madrid. A watan Oktoban 2012 ce ta haifa masa ’yar farko da suka rada mata suna Alba-biola.
Budurwar Gareth Bale ta sake haifar masa ’ya
A ranar Talatar da ta wuce ne shahararren dan kwallon Real Madrid na Sifen kuma haifaffen kasar Wales Gareth Bale ya baza hoton ’yar da…