Wani saurayi masoyin tsohon Gwamnan Jihar Kwankwasio daga Jihar Gombe Abdulrasheed Sa’id Bajoga, yana cigiyar budurwar nan ’yar a-mutun Kwankwaso da ta rabu da wanda zai aure ta saboda kiyayyarsa da Kwankwaso.
Abdulrasheed ya ce, matukar Lubna ta shirya ta kuma amince ta maye gurbin tsohon saurayin nata da shi, to ya a shirye yake a shafa musu fatiha.
- Na rabu da mai neman aurena kan raina Kwankwaso —Budurwa
- Kada a debe tsammani a kan ’yan matan Chibok — Zulum
- Yadda malaman Birnin Gwari suka tsere daga hannun ’yan bindiga
Matashin wanda shi ne Shugaban Kungiyar yada manufar siyasar Kwankwaso a kafafen sada zumunta, ya sanar da cigiyar Lubna ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Shugaban tsare-tsaren Kungiyar na kasa, reshen Jihar Gombe, Comrade Yusuf Dankanjiba
Sanarwar cigiyar ’yan a-mutun Kwankwson ta kuma karade shafuka da zaurukan sada zumunta na masoya da magoya bayan Sanata Kwankwaso.
Zan iya tarar mutuwa a kan Kwankwaso —Lubna
Lubna Ali, ta ce, a kan Kwakwaso za ta iya rasa ranta, kuma da ta auri wanda ba ya martaba shi, gara ta zauna har ababa ba ta yi aure ba.
“Na yi watsi da baikon manemin aurena saboda Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, duk da cewa Kwankwason ko sani na bai yi ba, amma a kansa zan iya karbar harsashi.
“Ba a matsayin dan siyasa kawai nake kallon Kwankwaso ba, a’a ina kallon sa ne a matsayin jagora, uba kuma abun koyi,” inji ta
Ta ce tun tana aji daya na Karamar Sakandare a shekarar 2003 take tsananin kaunar salon Kwankwason na tafiyar da lamuransa.
“Tun ban ma san me siyasa ke nufi ba, na haddace sunan Kwankwaso.
“Ba zan manta ba, motar da na fara mallaka ja ce kirar 406 kuma jikinta ko’in a like yake da hotunan Kwankwaso,” inji ta.