✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Budurwar da ta banka wa kanta wuta saboda saurayi ta rasu

Budurwa mai kimanin shekara 17 mai suna A’isha Aminu wanda ke zaune a Unguwar Albarkawa a garin Gusau a Jihar Zamfara da ta banka wa…

Budurwa mai kimanin shekara 17 mai suna A’isha Aminu wanda ke zaune a Unguwar Albarkawa a garin Gusau a Jihar Zamfara da ta banka wa kanta wuta saboda saurayinta ba ya da kudin aurenta a watan Satumba, ta rasu a safiyar yau Laraba.

Mahaifin A’isha, Malam Aminu Muhammad, ya bayyanawa Aminiya cewa, Aisha ta rasu ne yau bayan an yi mata wanka an maida ita gadon asibitin Cibiyar Lafiya ta Tarayya da ke garin Gusau inda take jinyar raunuka da ta samu sakamakon konewar da ta yi.

Malam Aminu, ya ce yau kwana 45 kenan suna jinyar Aisha tare da kashe kudaden magunguna a asibitin.

“Yau kwana biyu kenan aka bamu takardar sayan magunguna da ya kai akalla Naira dubu 26, amma babu kudin da zamu iya sayan magungunan.” Duk da yake jama’a nata tallafa mana da kudade lokacin da muke jinyar. Mun gode wa jamaa sosai.

Malam Aminu, ya kara da cewa an kashe sama da Naira dubu 700 akan wannan jinyar raunukan Aisha.